Ayu 6:24-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. “To, sai ku koya mini, ku bayyana mini laifofina,Zan yi shiru in kasa kunne gare ku.

25. Kila muhawara mai ma'ana ta rinjaye ni,Amma yanzu duk maganar shirme kuke yi.

26. Kuna so ku amsa maganganuna?Don me?Mutumin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi,Ba wata maganar da zai yi in ba shirme ba.

27. Kukan jefa wa bayi da marayu kuri'a,Kukan arzuta kanku daga abokanku na kurkusa.

Ayu 6