Ayu 6:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Da dutse aka yi ni?Ko da tagulla aka yi jikina?

13. Ba ni da sauran ƙarfi da zan ceci kaina,Ba inda zan juya in nemi taimako.

14. “A cikin irin wannan wahalaIna bukatar amintattun abokai,Ko da na rabu da Allah, ko ina tare da shi.

15. Amma ku abokaina,kun ruɗe ni,Kamar rafi wanda yakan ƙafe da rani.

16-17. Rafin yana cike da iska mai laima da ƙanƙara,Amma lokacin zafi sai su ɓace,Kwacciyar rafin, sai ta bushe ba kome.

18. Ayari sukan ɓata garin neman ruwa,Su yi ta gilo, har su marmace a hamada.

Ayu 6