6. Zunubi ba ya tsirowa daga ƙasa,Haka ma wahala ba ta tsirowa daga ƙasa.
7. Ai, an haifi mutum domin wahala ne,Tabbatacce ne kamar yadda tartsatsin wuta suke tashi.
8. “In da ni ne kai, da sai in juya wurin Allah,In kai ƙarata a wurinsa.
9. Ba za mu iya fahimtar manyan abubuwa da yake yi ba,Al'ajabansa kuwa ba su da iyaka.
10. Yakan aiko da ruwan sama,Ya shayar da gonaki.
11. I, Allah ne yake ɗaukaka masu tawali'u,Shi yake kuɓutar da dukan waɗanda suke makoki.
12. Yakan birkitar da shirye-shiryen masu wayo.
13. Yakan sa wa masu wayo tarko cikin dabarunsu,Har ba za su yi nasara a dukan abin da suke yi ba.
14. Da rana sukan yi karo da duhu,Ko da tsakar rana ma lalube suke kamar ana duhu.
15. Amma Allah yakan ceci matalauta daga mutuwa,Yakan kuma ceci masu bukata daga zalunci.
16. Yakan sa matalauta su sa zuciya,Ya sa mugaye su yi shiru.
17. “Mai farin ciki ne mutumin da Allah ya hora,Kada ka tsargu sa'ad da ya tsauta maka.
18. Allah yakan yi maganin raunin da ya yi maka,Ciwon da ya ji maka da hannunsa,Da hannunsa yakan warkar.
19. Yakan tsare ka daga cuta sau shida har sau bakwai,Ba muguntar da za ta taɓa ka.