20. Yakan kiyaye ka da rai a lokacin yunwa,A yaƙi kuma yakan tsare ka daga mutuwa.
21. Allah yakan kuɓutar da kai daga ƙarairayi da ɓata suna,Yakan cece ka daga hallaka.
22. Aikin kama-karya da yunwa za su zama abin dariya a gare ka,Ba kuwa za ka ji tsoron namomin jeji ba.
23. Ba za a sami duwatsu a gonakin da kake nomawa ba,Mugayen namomin jeji ba za su far maka ba.
24. Sa'an nan za ka zauna lafiya a alfarwanka,A sa'ad da ka dubi tumakinka, za ka tarar suna nan lafiya.
25. 'Ya'yanka za su yi yawa kamar ciyawa,Kamar yadda alkama take a lokacin kakarta.
26. Haka kai ma za ka rayu, har ka tsufa da kyakkyawan tsufa.