Ayu 41:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. “Ba zan yi shiru a kan zancen gaɓoɓinsa ba,Ko babban ƙarfinsa, ko kyan ƙirarsa.

13. Wa zai iya yaga babbar rigarsa?Ko kuwa ya kware sulkensa da aka ninka biyu?

14. Wa zai iya buɗe leɓunansa?Gama haƙoransa masu bantsoro ne.

15. An yi gadon bayansa da jerin garkuwoyi ne,An haɗa su daɓa-daɓa kamar an liƙe.

16. Suna haɗe da juna gam,Ko iska ba ta iya ratsa tsakaninsu.

17. Sun manne da juna har ba su rabuwa.

18. Atishawarsa takan walƙata walƙiya,Idanunsa kuma kamar ketowar alfijir.

Ayu 41