Ayu 39:27-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Ta wurin umarninka ne gaggafa take tashi samaTa yi sheƙarta can ƙwanƙoli?

28. A kan dutse take zaune, a can take gidanta,Cikin ruƙuƙin duwatsu.

29. Daga can takan tsinkayi abincintaIdanunta sukan hango shi tun daga nesa.

30. 'Yayanta sukan tsotsi jini,A inda kisassu suke, can take.”

Ayu 39