Ayu 37:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Numfashin Allah yakan sa ƙanƙara,Yakan sa manyan ruwaye su daskare farat ɗaya.

11. Yakan cika girgije mai duhu da ruwa,Gizagizai sukan baza walƙiyarsa.

12. Sukan yi ta kewayawa ta yadda ya bishe su,Don su cika dukan abin da ya umarce su a duniya da ake zaune a ciki.

Ayu 37