1. Elihu ya ci gaba da magana.
2. “Ka yi mini haƙuri kaɗan, ni kuwa zan nuna maka,Gama har yanzu ina da abin da zan faɗa in kāre Allah.
3. Zan tattaro ilimina daga nesa,In bayyana adalcin Mahaliccina.
4. Gaskiya nake faɗa ba ƙarya ba,Wanda yake da cikakken sani yana tare da kai.