Ayu 31:17-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ko kuwa in bar marayu da yunwa sa'ad da nake cin abincina,

18. Tun suna yara nake goyonsu,Ina lura da su kamar 'ya'yan cikina.

19. “Amma idan na ga wani yana lalacewa saboda rashin sutura,Ko wani matalauci marar abin rufa,

20. Idan a zuciyarsa bai sa mini albarka ba,Ko bai ji ɗumi da ulun tumakina ba,

21. Ko na ɗaga hannuna don in cuci maraya,Don na ga ina da kafar kuɓuta,

22. To, ka sa kafaɗuna su ɓaɓɓalle daga inda suke.Ka kakkarya gwiwoyin hannuna.

23. Gama bala'i daga wurin Allah ya razanar da ni,Saboda ɗaukakarsa ba zan iya yin kome ba.

24. “Idan na ce ga zinariya na dogara, ko zinariya tsantsa ita ce jigona,

25. Idan kuma saboda yawan dukiyata nake fariya,Ko saboda abin da na mallaka ne,

26. Idan ga hasken rana nake zuba ido,Ko ga hasken farin wata ne,

27. Zuciyata ta jarabtu ke nan a asirce,Ni da kaina ina sumbatar hannuna,

28. Wannan ma zai zama laifi ne wanda alƙalai za su hukunta,Gama na zama munafukin Allah Mai Iko Dukka ke nan.

29. “Idan na yi murna saboda wahala ta sami maƙiyana,Ko na yi fariya saboda mugun abu ya same shi,

30. Ban yi zunubi da bakina ba,Ban nemi ran wani ta wurin la'anta shi ba.

31. Ko mutanen da suke cikin alfarwata ba wanda zai ce,Ga wani can da bai ƙoshi da nama ba.

Ayu 31