Ayu 28:23-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. “Allah ne kaɗai ya san hanya zuwa gare ta,Ya san inda hikima take,

24. Saboda yana ganin duniya ɗungum,Yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sararin sama.

25. Sa'ad da Allah ya sa iska ta hura,Ya yi wa tekuna iyaka.

26. Sa'ad da ya ba da umarni ga ruwan sama,Da kuma hanyar da tsawa za ta bi,

Ayu 28