16. Ko da yake sun tsibe azurfa kamar turɓaya,Sun tara tufafi kamar ƙasa,
17. Za su tara, amma adalai za su sa,Marasa laifi ne za su raba azurfar.
18. Sun gina gidajensu kamar saƙar gizo-gizo,Kamar bukkar mai tsaro.
19. Attajirai za su kwanta, amma daga wannan shi ke nan,Za su buɗe ido su ga dukiyan nan ba ta.
20. Razana za ta auka musu kamar rigyawa.Da dare iska za ta tafi da su.
21. Iskar gabas za ta fauce su su tafi,Ta share su ta raba su da wurin zamansu.