Ayu 27:15-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Waɗanda suka tsira, annoba za ta kashe su,Matansu ba za su yi makokin mutuwarsu ba.

16. Ko da yake sun tsibe azurfa kamar turɓaya,Sun tara tufafi kamar ƙasa,

17. Za su tara, amma adalai za su sa,Marasa laifi ne za su raba azurfar.

18. Sun gina gidajensu kamar saƙar gizo-gizo,Kamar bukkar mai tsaro.

19. Attajirai za su kwanta, amma daga wannan shi ke nan,Za su buɗe ido su ga dukiyan nan ba ta.

Ayu 27