Ayu 25:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bildad ya amsa.

2. “Allah mai iko ne, duka sai a ji tsoronsa,A samaniya yake tafiya da mulkinsa da salama.

3. Akwai wanda zai iya ƙidaya mala'ikun da suke masa hidima?Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba?

4. Akwai wanda ya isa ya zama adali,Ko mai tsarki a gaban Allah?

5. Hasken wata ba haske ba ne a gare shi,Ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa.

Ayu 25