Ayu 23:13-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. “Bai taɓa sākewa ba. Ba wanda zai iya gāba da shi,Ko kuma ya hana shi yin abin da yake so ya aikata.

14. Zai tabbatar da abin da ya shirya domina,Wannan ma ɗaya daga cikin shirye-shiryen da ya yi ne.

15. Don haka in rawar jiki a gabansa saboda tsoro.

16. Allah Mai Iko Dukka ya lalatar da ƙarfin halina.Allah ne ya tsorata ni,

Ayu 23