Ayu 21:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ku ba ni zarafi in yi magana, sa'an nan in na gama ku amsa in kun ga dama.

4. “Ba da 'yan adam nake faɗa ba,Ina da isasshen hanzarin da zai sa in yi fushi.

5. Ku dube ni, ashe, wannan bai isa ya sa ku yi zuru,Ku firgita, ku yi shiru ba?

6. Sa'ad da na tuna da abin da ya same ni,Sai jikina ya yi suwu, in yi ta makyarkyata ina rawar jiki.

7. Me ya sa Allah yake barin mugayeHar su tsufa su kuma yi arziki?

8. 'Ya'yansu da jikokinsu sukan girma a idonsu.

9. Allah bai taɓa aukar wa gidajensu da bala'i ba,Ba su taɓa zama a razane ba.

10. Hakika shanunsu suna ta hayayyafa,Suna haihuwa ba wahala.

11. 'Ya'yansu suna guje-guje,Suna tsalle kamar 'yan raguna,

12. Suna rawa ana kaɗa garaya,Ana busa sarewa.

13. Suka yi zamansu da salama,Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.

14. Mugaye sukan ce wa Allah ya ƙyale su kurum,Ba su so su san nufinsa game da hanyoyinsu.

15. Suna tsammani ba amfani a bauta wa Allah,Ko a yi addu'a gare shi domin samun wata fa'ida.

Ayu 21