Ayu 21:12-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Suna rawa ana kaɗa garaya,Ana busa sarewa.

13. Suka yi zamansu da salama,Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.

14. Mugaye sukan ce wa Allah ya ƙyale su kurum,Ba su so su san nufinsa game da hanyoyinsu.

15. Suna tsammani ba amfani a bauta wa Allah,Ko a yi addu'a gare shi domin samun wata fa'ida.

Ayu 21