Ayu 21:11-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. 'Ya'yansu suna guje-guje,Suna tsalle kamar 'yan raguna,

12. Suna rawa ana kaɗa garaya,Ana busa sarewa.

13. Suka yi zamansu da salama,Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.

14. Mugaye sukan ce wa Allah ya ƙyale su kurum,Ba su so su san nufinsa game da hanyoyinsu.

15. Suna tsammani ba amfani a bauta wa Allah,Ko a yi addu'a gare shi domin samun wata fa'ida.

16. Sukan ce ta wurin ƙarfinsu ne suka yi nasara,Amma ban yarda da irin tunaninsu ba.

17. “An taɓa kashe hasken mugun mutum?Ko masifa ta taɓa fāɗa wa wani daga cikinsu?Allah ya taɓa hukunta wa mugu da fushi,

18. Ya kuma sa su zama kamar tattakar da iska yake kwashewa?Ko kuma kamar ƙura wadda hadiri yake kwashewa?

19. “Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa.A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi.Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.

20. Bari dai a hukunta masu zunubiSu kuma ga hasalar Allah.

21. Bayan rasuwar mutum,Ruwansa ne ya sani ko 'ya'yansa suna jin daɗi?

22. Mutum zai iya koya wa Allah?Mutum zai iya shara'anta wa Allah Mai Iko Dukka?

23. “Waɗansu mutane sukan yi zamansu ba ciwon kome har ranar mutuwarsu,Suna cikin farin ciki da jin daɗi,

24. Jikunansu kuwa sun yi ɓulɓul.

25. Waɗansu kuwa ba su taɓa sanin farin ciki ba.Sukan yi dukan kwanakinsu su mutu da baƙin ciki.

26. Amma duk abu guda ne su, mutuwa za su yi, a binne,Tsutsotsi su lulluɓe su duka.

27. “Na san irin tunaninku na hassada,

28. Kuna ta tambaya, ‘Ina ne gidan babban mutumin nan yanzu,Wato mutumin da yake aikata mugunta?’

29. “Ashe, ba ku yi magana da matafiya ba?Ba ku kuma san rahoton da suka kawo ba?

Ayu 21