Ayu 21:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Hakika shanunsu suna ta hayayyafa,Suna haihuwa ba wahala.

11. 'Ya'yansu suna guje-guje,Suna tsalle kamar 'yan raguna,

12. Suna rawa ana kaɗa garaya,Ana busa sarewa.

13. Suka yi zamansu da salama,Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.

Ayu 21