5. Amma yanzu da a ce za ka taɓa lafiyar jikinsa, da sai yă fito fili yă zage ka.”
6. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Shi ke nan, yana cikin ikonka, amma fa, kada ka kashe shi.”
7. Sa'an nan Shaiɗan ya rabu da Ubangiji, ya je ya sa ƙuraje su fito ko'ina a jikin Ayuba.
8. Ayuba ya je ya zauna kusa da juji ya ɗauki tsingaro ya yi ta sosa ƙurajen.
9. Sai matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana da amincin nan naka? Don me ba za ka zagi Allah ka mutu ba?”
10. Ayuba ya amsa, ya ce mata, “Wace irin maganar gāɓanci ce haka? Lokacin da Allah ya aiko mana da alheri, mukan yi na'am da shi, to, me zai sa sa'ad da ya aiko mana da wahala za mu yi gunaguni?” Cikin dukan wahalar da Ayuba ya sha, bai sa wa Allah laifi ba.