Ayu 17:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Yanzu kuwa sun mai da wannan karin magana a kaina.Da mutane suka ji,Suka zo suka yi ta tofa mini yau a fuska.

7. Baƙin cikina ya kusa makantar da ni,Hannuwana da ƙafafuna sun rame,sun zama kamar kyauro.

8. Duk waɗanda suka zaci su adalai ne sun razana.Dukansu sun kāshe ni, cewa ni ba mai tsoron Allah ba ne.

9. Har su ma da suke cewa su mutanen kirki neSuna ƙara tabbatarwa ba su yi kuskure ba.

10. Amma da a ce dukansu za su zo su tsaya a gabana,Da ba zan sami mai hikima ko ɗaya daga cikinsu ba.

Ayu 17