13. Ba ni da sauran sa zuciya,Gidana yana lahira,Inda zan kwanta in yi ta barci cikin duhu.
14. Zan ce kabari shi ne mahaifina,Tsutsotsin da suke cinye ni su ne mahaifiyata, da 'yan'uwana mata.
15. Ina ne zan sa zuciyata?Wane ne ya ga inda zan sa ta?