Ayu 11:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Kana iya gane matuƙa da iyakarGirman Allah da na ikonsa?

8. Sararin sama ba shi ne matuƙa a wurin Allah ba,Amma ga shi, yana can nesa da kai,Allah ya san lahira,Amma kai ba ka sani ba.

9. Fāɗin girman Allah ya fi duniyaYa kuma fi teku fāɗi.

10. Idan Allah ya kama ka ya gurfanar da kai gaban shari'a,Wa zai iya hana shi?

11. Allah ya san irin mutanen da ba su da amfani,Domin yana ganin dukan mugayen ayyukansu.

12. Idan dakikan mutane sa yi hikima,To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida.

13. “Ayuba, ka shirya zuciyarka,Ka ɗaga hannuwanka zuwa wurin Allah.

14. Ka kawar da mugunta da kuskure daga gidanka.

15. Sa'an nan ka sāke shan ɗamarar zaman duniya,Da ƙarfi da rashin tsoro.

16. Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka,Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita.

Ayu 11