Ayu 11:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Allah ya san irin mutanen da ba su da amfani,Domin yana ganin dukan mugayen ayyukansu.

12. Idan dakikan mutane sa yi hikima,To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida.

13. “Ayuba, ka shirya zuciyarka,Ka ɗaga hannuwanka zuwa wurin Allah.

14. Ka kawar da mugunta da kuskure daga gidanka.

15. Sa'an nan ka sāke shan ɗamarar zaman duniya,Da ƙarfi da rashin tsoro.

16. Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka,Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita.

17. Ranka zai yi haske fiye da hasken rana da tsakar rana.Kwanakin ranka mafiya duhuZa su yi haske kamar ketowar alfijir.

18. Za ka yi zaman lafiya, cike da sa zuciya,Allah zai kiyaye ka, ya ba ka hutawa.

Ayu 11