1. Zofar ya amsa.
2. “Ba wanda zai amsa dukan wannan surutu?Yawan magana yakan sa mutum ya zama daidai?
3. Ayuba,kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba?Kana tsammani maganganunka na ba'aZa su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?
4. Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne,Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah.