Ayu 10:20-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Raina bai kusa ƙarewa ba? A bar ni kawai!Bari in ci moriyar lokacin da ya rage mini.

21. An jima kaɗan zan tafi, ba kuwa zan komo ba faufau,Zan tafi ƙasa mai duhu, inda ba haske,

22. Ƙasa mai duhu, da inuwoyi da ɗimuwaInda ko haske ma kansa duhu ne.”

Ayu 10