5. A kowane lokacin da aka gama da liyafar, Ayuba yakan tashi da sassafe, kashegarin liyafar, yă miƙa hadayu don yă tsarkake 'ya'yansa. Haka yake yi kullum, don yana zaton mai yiwuwa ne ɗaya daga cikin 'ya'yan ya yi zunubi, ya saɓi Allah a ɓoye.
6. Sa'ad da ranar da talikan sama masu rai sukan hallara gaban Ubangiji ta yi, Shaiɗan ma ya zo tare da su.
7. Sai Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Kai fa me kake yi?”Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Ina ta kaiwa da kawowa ne, a ko'ina a duniya.”
8. Ubangiji ya ce masa, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.”
9. Shaiɗan ya amsa, ya ce, “A banza Ayuba yake yi maka sujada?
10. Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasan nan.