1. Akwai wani mutum a ƙasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.
2. Yana da 'ya'ya bakwai maza, uku mata.
3. Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da raƙuma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki nesa.