A.m. 24:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Da mai mulki ya alamta wa Bulus ya yi magana, sai ya amsa ya ce, “Tun da na sani ka yi shekaru da yawa kana yi wa jama'ar nan shari'a, da farin ciki zan kawo hanzarina.

11. Ai, ka iya tabbatarwa, bai fi kwana goma sha biyu ba tun da na tafi Urushalima yin sujada.

12. Ba su kuwa taɓa samuna ina muhawwara da kowa ba, ko kuwa ta da husuma har mutane su taru a Haikali, ko a majami'u, ko kuwa a cikin birni.

13. Ba kuma za su iya tabbatar maka abin da yanzu suke ƙarata a kai ba.

14. Amma na yarda cewa, bisa ga hanyar nan da suke kira ‘Ɗariƙa’ nake bauta wa Allahn kakanninmu, nake kuma gaskata duk abin da yake a rubuce a cikin Attaura da kuma littattafan annabawa.

15. Ina sa zuciya ga Allah, yadda su waɗannan ma suke sawa, wato za a ta da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.

16. Saboda haka, a kullum nake himma in kasance da lamiri marar abin zargi a wurin Allah da wurin mutane.

17. To, bayan 'yan shekaru sai na je domin in kai gudunmawa ga jama'armu, in kuma yi sadaka.

18. Ina cikin yin haka sai suka same ni a tsarkake a Haikali, ba kuwa da wani taro ba, balle hargowa. Amma akwai waɗansu Yahudawa daga ƙasar Asiya–

A.m. 24