5. Babban firist ma da dukan majalisar shugabannin jama'a za su iya shaidata, daga gunsu ne kuma na karɓi wasiƙu zuwa ga 'yan'uwanmu Yahudawa, na tafi Dimashƙu, don in ɗebo waɗanda suke can ma, in zo da su Urushalima a ɗaure, a azabta su.”
6. “Ina cikin tafiya, da na yi kusa da Dimashƙu, wajen rana tsaka, kwamfa sai wani matsanancin haske ya bayyano daga sama, ya haskaka kewaye da ni.
7. Sai na fāɗi, na kuma ji wata murya tana ce mini, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?’
8. Ni kuma na amsa na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ Sai ya ce mini, ‘Ni ne Yesu Banazare wanda kake tsananta wa.’
9. To, waɗanda suke tare da ni sun ga hasken, amma ba su ji kalmomin mai yi mini maganar nan ba.