A.m. 22:28-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Sai shugaban ya amsa ya ce, “Ni fa da kuɗi masu yawa na sami 'yancin nan.” Bulus ya ce, “ni kuwa da shi aka haife ni.”

29. Saboda haka, waɗanda suke shirin tuhumarsa, suka rabu da shi nan da nan. Shi ma shugaban da ya fahimci Bulus Barome ne, sai ya tsorata, ga shi kuwa, ya ɗaure shi.

30. Kashegari kuma da shugaban ya so sanin ainihin ƙarar da Yahudawa suke yi a kan Bulus, sai ya kwance shi, ya yi umarni manyan firistoci da dukan majalisa su taru, sa'an nan ya sauko da Bulus ya tsai da shi a gabansu.

A.m. 22