6. Sai muka shiga jirgi, su kuma suka koma gida.
7. Da muka gama tafiyarmu daga Taya, muka isa Talamayas, muka gaisa da 'yan'uwa, muka kuma kwana ɗaya a wurinsu.
8. Kashegari muka tashi muka zo Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai yin bishara, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa.
9. Shi kuwa yana da 'ya'ya huɗu 'yan mata, masu yin annabci.
10. To, muna nan zaune 'yan kwanaki, sai wani annabi, mai suna Agabas, ya zo daga Yahudiya.
11. Da ya zo gare mu, ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sawu da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga al'ummai.’ ”
12. Da muka ji haka, mu da waɗanda suke wurin muka roƙi Bulus kada ya je Urushalima.
13. Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”
14. Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Ubangiji ya yi yadda ya so.”
15. Bayan 'yan kwanakin nan muka shirya muka tafi Urushalima.