34. Ku da kanku kun sani hannuwan nan nawa su suka biya mini bukace-bukacena, da na waɗanda suke tare da ni.
35. Na zamar muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta wahalar aiki haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”
36. Da Bulus ya faɗi haka, ya durƙusa, duka suka yi addu'a tare.