A.m. 14:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, a Ikoniya suka shiga majami'ar Yahudawa tare, suka yi wa'azi, har mutane masu yawa, Yahudawa da al'ummai, suka ba da gaskiya.

2. Amma Yahudawa da suka ƙi bi, suka zuga al'ummai, suka ɓata tsakaninsu da 'yan'uwa.

A.m. 14