39. Mu kuwa shaidu ne ga duk abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da Urushalima. Shi ne kuma suka kashe ta wurin kafa shi a jikin gungume.
40. Shi ne Allah ya tasa a rana ta uku, ya kuma yarda ya bayyana,
41. ba ga dukan jama'a ba, sai dai ga shaidun nan da Allah ya zaɓa tun dā, wato mu ke nan, da muka ci muka sha tare da shi, bayan ya tashi daga matattu.
42. Ya kuma umarce mu mu yi wa mutane wa'azi, mu kuma tabbatar cewa shi ne wanda Allah ya sa mai hukunta rayayyu da matattu.
43. Shi ne duk annabawa suka yi wa shaida, cewa albarkacin sunansa duk mai gaskatawa da shi zai sami gafarar zunubai.”