24. ku ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.
25. Saboda haka, sai ku watsar da ƙarya, kowa yă riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa, gama mu gaɓoɓin juna ne.
26. In kun husata, kada ku yi zunubi, kada ma fushinku ya kai faɗuwar rana,
27. kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa.
28. Kada ɓarawo ya ƙara yin sata, a maimakon haka sai ya motsa jiki yana aikin gaskiya da hannunsa, har da zai sami abin da zai ba matalauta.