Afi 4:20-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ba haka kuka koyi al'amarin Almasihu ba,

21. in da a ce kun saurare shi, an kuma koya muku ta gare shi ne, wato yadda gaskiya ta Yesu take.

22. Ku yar da halinku na dā, wanda dā kuke a ciki, wanda yake lalacewa saboda sha'awoyinsa na yaudara,

23. ku kuma sabunta ra'ayin hankalinku,

Afi 4