3. wato yadda aka sanar da ni asirin Ubangiji ta wahayi, kamar yadda na riga na rubuta a taƙaice.
4. A yayin da kuka karanta wannan, za ku iya gane basirata saboda asirin Almasihu,
5. wanda a zamanin dā ba a sanar da 'yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu,
6. wato, yadda ta wurin bishara al'ummai da suke abokan gādo da mu, gaɓoɓin jiki guda, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Almasihu Yesu.