21. a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma.
22. Allah kuma ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikon Almasihu, ya kuma ba da shi ga Ikkilisiya ya zama Kai mai mallakar abu duka.
23. Ikkilisiya ita ce jikin Almasihu, cikar mai cika dukkan abu.