Sulemanu kuwa ya kawo 'yar Fir'auna daga birnin Dawuda zuwa gidan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za ta zauna a gidan Dawuda, Sarkin Isra'ilawa ba, saboda duk wuraren da akwatin Ubangiji ya shiga sun tsarkaka.”