2 Tar 5:13-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Ya zama aikin mabusan ƙaho ne, da mawaƙa duka, su haɗa kai, har a ji su suna yabon Ubangiji, suna godiya, sa'ad da suka ɗaga waƙa daidai da muryar ƙaho da ta kuge, da dukan kayan bushe-bushe suka yi ta raira waƙa cewa,“Yabo ya tabbata ga UbangijiGama shi nagari ne,Ƙaunarsa kuwa madawwamiya ce.”Gidan kuwa, wato Haikalin Ubangiji, ya cika da girgije,

14. har ma firistoci ba su iya tsayawa su ci gaba da hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Allah.

2 Tar 5