2 Tar 5:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sulemanu ya kammala dukan aikin Haikalin Ubangiji. Sa'an nan ya kawo kayayyakin da tsohonsa Dawuda ya riga ya keɓe, wato azurfa da zinariya, da dukan kayan girke-girke, da tasoshi, ya ajiye su a taskokin Haikalin Allah.

2. Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama'ar Isra'ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona.

3. Sai dukan mutanen Isra'ila suka hallara a gaban sarki, a wurin bikin, a wata na bakwai ke nan.

4. Sa'an nan dukan dattawan Isra'ila suka zo, Lawiyawa kuwa suka ɗauko akwatin.

2 Tar 5