17. Sarki ya yi zubinsu a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zaretan a wuri mai yumɓu.
18. Haka Sulemanu ya yi kayayyakin nan da yawa ƙwarai, har ba a iya lissafin yawan nauyin tagullar da aka yi amfani da ita ba.
19-22. Haka kuwa Sulemanu ya yi dukan kayayyakin nan da suke cikin Haikalin Allah, duk da zinariya tsantsa aka yi su.bagade na zinariyatebur don ajiye gurasar ajiyewaalkukai tare da fitilunsu na zinariya tsantsa, domin a kunna su a gaban Wuri Mafi Tsarki na ciki kamar yadda aka tsarafurannifitiluarautakihantsukadarunacokulafarantan wutaƙofofi na can cikiƙofofi na waje