Ya miƙa 'ya'yansa maza hadaya ta ƙonawa a kwarin ɗan Hinnom. Ya yi bokanci, ya yi duba, ya yi tsubbu, yana kuma sha'ani da makarai da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanar fushin Ubangiji.