2 Tar 32:31-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. A kan 'yan saƙon sarakunan Babila kuwa, waɗanda aka aiko su don su bincika irin abin al'ajabi da ya faru a ƙasar, sai Allah ya ƙyale shi kurum don ya jarraba shi, ya san dukan abin da suke a zuciyarsa.

32. Sauran ayyukan Hezekiya da kyawawan ayyukansa, ga shi, an rubuta su a wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila.

33. Sai Hezekiya ya rasu, suka binne shi a sashe na bisa na hurumin 'ya'yan Dawuda, maza. Dukan Yahuza da mazaunan Urushalima suka girmama shi sa'ad da ya rasu. Sai Manassa ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.

2 Tar 32