2 Tar 30:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Suka yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Suka sa firistoci da Lawiyawa su sha kunya, saboda haka sai suka tsarkake kansu, suka kawo hadayu na ƙonawa a Haikalin Ubangiji.

16. Sai suka ɗauki matsayinsu wanda aka ayyana bisa ga dokar Musa, mutumin Allah, firistocin suka yarfa jinin da suka karɓa daga hannun Lawiyawa.

17. Gama akwai waɗansu da yawa daga cikin taron waɗanda ba su tsarkake kansu ba, saboda haka ya zama tilas Lawiyawa su yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa saboda dukan wanda ba shi da tsarki, domin a tsarkake shi ga Ubangiji.

18. Gama akwai jama'a jingim, da yawa kuwa mutanen Ifraimu ne, da na Manassa, da na Issaka, da na Zabaluna, da ba su tsarkake kansu ba, duk da haka sun ci Idin Ƙetarewa ba yadda aka ƙayyade ba. Sai Hezekiya ya yi addu'a dominsu, yana cewa, “Ya Ubangiji mai alheri, ka gafarta wa ko wanne

19. wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko bai yi bisa kan dokar tsarkakewa na Wuri Mai Tsarki ba.”

20. Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya, ya warkar da jama'ar.

21. Jama'ar Isra'ila waɗanda suke a Urushalima kuwa sun yi idin abinci marar yisti da murna mai yawa, har kwana bakwai. Lawiyawa kuma da firistoci suka yabi Ubangiji kowace rana, suna raira waƙa da iyakar ƙarfinsu ga Ubangiji.

2 Tar 30