Sulemanu fa ya aika wurin Hiram Sarkin Taya ya ce, “Yadda ka yi wa tsohona Dawuda, wato ka aiko masa da itatuwan al'ul domin ya gina gida inda zai zauna, ni ma ina so ka yi mini haka.