32. Da shugabannin karusai suka ga, ashe, ba Sarkin Isra'ila ba ne, sai suka daina binsa suka juyo.
33. Amma wani mutum ya harba kibiya haka kawai, ya sami Sarkin Isra'ila a mahaɗin kafaɗa. Sai sarkin ya ce wa wanda yake korar karusarsa, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin, gama an yi mini rauni.”
34. Ran nan yaƙin ya tsananta, Sarkin Isra'ila kuma ya jingina a cikin karusarsa, yana fuskantar Suriyawa har maraice, rana na fāɗuwa yana rasuwa.