11. Ayyukan Asa, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a littafin sarakunan Yahuza da na Isra'ila.
12. A shekara ta talatin da tara ta mulkin Asa, sai wani ciwo ya kama shi a ƙafa. Ciwon kuwa ya tsananta ƙwarai, duk da haka Asa bai nemi taimakon Ubangiji ba, sai na magori.
13. Asa fa ya rasu bayan shekara biyu da ciwon, a shekara ta arba'in da ɗaya ta mulkinsa.
14. Aka binne shi a kabarin da shi da kansa ya haƙa a birnin Dawuda. Aka sa shi a makara wadda aka cika da kayan ƙanshi da na turare yadda gwanayen aikin turare suka shirya, suka hura babbar wuta don su darajanta shi.