2 Tar 11:8-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. da Gat, da Maresha, da Zif,

9. da Adorayim, da Lakish, da Azeka,

10. da Zora, da Ayalon, da Hebron. Waɗannan su ne birane masu kagara a Yahuza da Biliyaminu.

11. Ya kuma ƙara ƙarfin kagaran, ya sa sarakunan yaƙi a cikinsu. Ya tara abinci, da mai, da ruwan inabi a cikinsu.

12. Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen nan, ya ƙara musu ƙarfi ƙwarai. Haka ya riƙe Yahuza da Biliyaminu.

13. Firistoci da Lawiyawa da suke a dukan Isra'ila kuwa suka komo gare shi daga dukan wuraren da suke.

14. Sai Lawiyawa suka bar makiyayarsu da dukiyarsu, suka koma Yahuza da Urushalima, saboda Yerobowam da 'ya'yansa maza sun hana su yi hidimarsu ta firistocin Ubangiji.

2 Tar 11