Rehobowam ya fi ƙaunar Ma'aka, 'yar Absalom, fiye da dukan matansa, da ƙwaraƙwaransa. Yana kuwa da matan aure goma sha takwas, da ƙwaraƙwarai sittin. 'Ya'yan da ya haifa maza ashirin da takwas ne, 'ya'ya mata kuwa sittin.